Wannan lamarin ya sa kakakin majalisar na lokacin Ahmed Umar Fintiri ya dare kujerar gwamna kafin daga bisani kotu ta saukar dashi ta nada James Nigilari a a matsayin gwamnan da har yanzu yana kan karagar mulki.
Tun lokacin da kotu ta tsayar da James Ngilari a matsayin gwamnan jihar takaddama ta cigaba da yin tsamari tsakanin bangaren zartaswa da na majalisar dokoki. Bangarorin suna zargin juna da yin sama da fadi da yin ruf da ciki da dukiyoyin jama'a..
Lamarin ya kawo cikas a jihar domin tamkar ayyukan gwamnati sun tsaya cak. Sabili da haka wasu kungiyoyi masu kishin jihar sun soma sa baki a takaddamar. Kungiyar da ake kira Adamawa Progressive Movement a karkashin shugabancin Barrister Sunday Joshua Wagira tana zargin kakakin majalisar dokokin jihar Ahmed Fintiri da yin almubazaranci da kudi nera biliyan 22 a cikin kwanaki 86 kacal da ya yi mulkin kasar kan kwagiloli na bogi.
Kungiyar tace ya bayar da kwangiloli a wuraren da 'yan Boko Haram suka mamaye sabili da haka babu komi a rubuce ko kuma alamar aikin da aka yi. Yace dole Fintiri ya yiwa jama'ar jihar bayani.
Solomon Kurangar jami'in yada labarai na Ahmed Fintiri ya mayarda martani inda yace bita da kuli ne kawai ake yiwa kakakin ganin cewa cikin dan karamin lokacin da yayi yana gwamna ya yi aiki tare da biyan ma'aikatan jihar albashin watanni biyu, kudin da gwamnatin Nyako ta ki biyansu. Ya kara da cewa kudaden da ake zargi ya kashe suna nan a ma'aikatar aiki ta jiha
Ga rahoton Sanusi Adamu
..