Wasu kusoshin jam'iyyar hamayya ta PDP a shiyar arewa maso gabas suna yabawa da yadda shugaban kasa ke yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya.
'Yan yankin sun ce abun takaici ne a ce da hannun wasu daga yankinsu cikin badakalar kudaden sayan makaman yaki da Boko Haram musamman ganin cewa yankin ne rikicin na Boko Haram ya fi daidaitawa..
Alhaji Muhammad Baba Amin na Adamawa wani kusa ne a jam'iyyar PDP a jihar.Yace bai kamata a hada duk 'yan jama'iyyar cikin badakalar ba domin ba duka 'yan PDP ke da hannu cikin badakalar ba.Duk da cewa suna nan daram cikin jam'iyyar daram amma zasu cigaba da goyon bayan fafutikar yaki da cin hanci da rashawa da shugaba Buhari ke yi.
Yace su yanzu zasu gyarajam'iyyarsu kuma duk wanda yake da hannu a badakalar a hukuntashi.Yace suna nan da yawa cikin jam'yyar da basu san abubuwan da suka faru ba. Ya kira a yi bincike tsakani da Allah. Abun takaici ne a ce Alex Badeh tsohon hafsan hafsoshin sojojin Najeriya da ya fito daga yankinsu ya gaza har ma watakila da hannunsa a badakalar.
Tuni ma wassu suke kira akafa kotu na musamman da zai yi shari'ar badakalar. To saidai wasu masana shari'a nada ra'ayi daban Idris.Abdullahi Jalo na kungiyar lauyoyin Taraba yana ganin ba dole sai an yi hakan ba muddin masu shari'a zasu yi adalci.
Ga karin bayani.