Ana cewa idan kana yaki da cin hanci itama zata yake ka tabbas haka ne a’i, bazaka zage kana fada da wani batare da shima yayi fada da kai ba, muyi kudiri muyi azama sannan mun shirta tsafe domin cin nasara a wanna yaki da cin hanci.
Shugaban hukumar ta EFCC, ya bayyana cewar indai gwagwarmayar yaki da cin hanci a Najeriya ne koda zai rasa ransa shi ya shirya.
“Saboda ‘yan Najeriya, sama da miliyan 70, tunda har na sami damar bada tawa gudunmawar na yakar cin hanci da rashawa da laifukan da suka shafi kudi dama yadda ake halarta kudi haram a Najeriya, koda a kokarin wanna yakin zan rasa rai na toh na shirya.”
Shugaban hukumar ta EFCC Ibrahim Mustapha Magu, ya kuma tabo batun tuhumar da sukewa tsohon shugaban hukumar sifiri ruwa ta Najeriya, wato NIMASA, Ziakede Patrick Akpobolekemi,misali kamar badakalar da aka tafka a hukumar sifirin ruwa ta NIMASA, alokacin da muka kai shi kotu batun ne na wawure Naira miliya, 2,000, amma daga bisa muka kara bankado wata sabuwar badakalar na wawure Naira miliyan 34,000, daga dukiyar talakawan Najeriya, saboda akwai dalilai da dama dake sa muke wasu abubuwa muna bincike ne ta karkashin kasa.
Wani mai rajin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, Mr. Abraham Unaji, yace idan har aka yi nasara akan yaki da cin hanci da rashawa toh tabbaci hakika komai zai yi dai dai.