Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kisa, Dauri Ko Datse Hannu Ya Dace Akan Al'mundahana a Najeriya


EFCC
EFCC

Jama’a da masana suna ta ci gaba da tofa albarkacin bakinsu game da dimbin dukiyar Najeriya da aka sha yin sama da fadi da ita, sakamakon kuruciyar bera da wasu shugabannin kasar ke aikatawa.

Shugaban rundunar adalci a Najeriya Alhaji Abdulkarim Dayyabu a hirarsa da abokiyar aikinmu Grace Alheri Abdu ya bayyana cewa, yana ganin ya kamata a fara yanke hukuncin da in ma ta kama a harbe ko a daure, kai har ma in ta kama a datsewa wasu hannuwa.

Ya kawo misalin yadda tsohuwar shugabar hukumar yaki da almundahana da dukiyar kasa ta EFCC wato Farida Waziri, da ta taba bada shawarar ya kamata a dinga duba kwakwalen masu mulki kafin a basu damar shugabanci.

A karshe ma dai Abdulkarim Dayyabun yana ganin abinma dai da ya fi dacewa a koma kawai kwatankwacin hukuncin da irinsu China ke yi, ko da kuwa za’a canza Kundin tsarin mulkin Najeriyar ne.

Domin kuwa ya karkare da cewa, barnar da aka yiwa kasar ta sace dukiyar kasar ba ma zata kidayu da baki ba, don haka Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ba siddabaru gareshi da zai canza komai dare day aba, sai da sa hannun ‘yan Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:05:16 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG