Wani dan rajin yaki da almundahana a jahar Bauchi ya gamu da fushin hukuma saboda abin da wasu da dama ke ganin takura ma hukumar ya yi.
Sakataren kungiyar masu yaki da almubazzaranci da dukiyar al’umma Alhaji Yakubu Jibrin, wanda kan yi rubuce rubuce kan abubuwan da su ka shafi zarge zargen cin kudin jama’a, ya fada ragar yan sanda ne bayan da ya rubuta wata takardar zargin handamar kudaden jama’a da ya yi ma gwamnatin Bauchi.
An dai kama shugaban kungiyar “Bauchi Coalition Against Financial Crime and Injustice” din ne a gidansa, al’amarin da ya janyo cece ku ce daga jama’a, wadanda ke ganin ba a masa adalci ba.
To amma kakakin Hukumar ‘Yansandan Jahar Bauchi, Sufuritanda Haruna Muhammad y ace an kama Alhaji Yakubu ne a matsayin wanda ake zargi, don haka ba a daukarsa a matsayin wanda ya aikata laifi har sai kotu ta yanke hukunci kan zargin kagen da gwamnati ta yi masa. Gwamnatin ta kuma zarge shi da yinkurin tayar da fitina.
Ga wakilinmu a Bauchi Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton: