Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rigimar Siyasa: Tsohon Gwamna Kure Ya Tsallake Rijiya Da Baya


Sufeto-Janar na 'Yansandan Najeriya Solomon Arase
Sufeto-Janar na 'Yansandan Najeriya Solomon Arase

Rundunar 'Yansandan Jahar Naija ta tabbatar da bugawar da PDP da APC su ka yi a garin Suleja, inda har aka samu raunuka.

Tsohon Gwamnan jahar Naija Injiniya Abdulkadir Kure da mukarrabansa sun tsallake rijiya da baibai, baya ga mutune 9, ciki har da ‘yansanda 5, da su ka jijji raunuka a wata bugawar da aka yi a garin Suleja tsakanin ‘yan jam’iyyar PDP ta adawa da jam’iyyar APC mai mulki.

Wannan fafatawar ta biyo bayan yakin neman zabe ne da jam’iyyar PDP, karkashin tsohon gwamnan ta je yi a Sulejan game da zabukan kananan hukumomin da za a yi ranar Asabar mai zuwa. Jam’iyyar PDP ta zargi Danmajalisar Wakilan Najeriya Alhaji Lado Suleja da ingiza wadanda su ka far masu din, kamar dai yadda mataimakin Shugaban jam’iyyar PDP, Barrister Tanko Beji, ya yi zargi.

Jami’in yada labarai na Rundunar ‘Yansandan Jahar Naija, ASP Bala Elkana, ya tabbatar cewa yayin da PDP ke gangami, shi kuma Bala Lado mai tafe da magoya bayansa, sai su ka yi karo a hanya, inda aka raunata mutane har da DPO na ‘yansanda. To amma APC ta bakin Lado, ta ce sam ba ita ta haddasa rigimar ba.

Ga dai wakilnmu a Naija Mustapha Nasiru Batsari da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG