Hukumar binciken zata bude wani sabon babin yadda aka kashe wasu makudan kudade da suka hada da kudin Euro miliyan uku da dubu dari shida da hamsin da hudu da dari daya da ashirin da daya.
Wai an yi anfani da kudaden ne an sayi motocin sulke da aka ba wata kasa dake makwaftaka da kasar a shekarar 2013 da 2014.
Kakakin hukumar EFCC Mr. William Uwajere ya ki ya ce komi a kan maganar domin wai ana kan bincike.
Kwamred Abdulsalami Abubakar jami'i a wata kungiya dake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya yace kamata yayi a ware kotu ta musamman da zata yi masu shari'a ba irin kotun dake sakesu suna zuwa beli ba ana kai komo kullum. Ya kamata ma a mai da hukuncin kisa kan duk wanda aka sameshi da laifi.
Ana kyautata zaton nan da dan lokaci kadan hukumar ta EFCC zata gayyato wasu manyan hafsoshin sojojin kasar akan badakalar domin su bada nasu bahasi. Kazalika hukumar zata bude wani sabon bincike akan yadda Sambo Dasuki ya yi anfani da wasu dalar Amurka miliyan 332 da ya karba a ma'aikatar kudi ta gwamnatin Goodluck Jonathan.
Ga karin bayani.