Gwamnati ta shaidawa kasar cewaa zata sayo kayan yaki ne da kudaden saboda dakarun kasar su samu su shawo kan 'yan tsagerar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
An raba kudaden ne kashi kashi ma wasu manyan 'yan siyasan Najeriya .
Tsohon shugaban kwamitin amintattun PDP Tony Anenih shi ya fada haka lokacin da yake yiwa hukumar EFCC karin bayani dangane da abun da yayi da makudan kudin da ya karba hannun Kanar Sambo Dasuki mai ba shugaban kasa na wancan lokacin shawara kan harkokin tsaro. Tony Anenih yace ya ba Alhaji Tanko Yakasai nera miliyan sittin da uku ko N63m.
To amma shi Alhaji Tanko Yakasaiyana da nashi bayanin. Yace bashi Tank Yakasai aka ba kudin ba shi kadai. Kwamitin da aka kafa ya zagaye jihohin arewa ya gana da manyan sarakuna, ya rokesu a yi zabe lafiya aka ba kudin.
Yace an basu kudin ne su biya ma kansu kudin tafiya da biyan wuraren kwana da biyan kudin abinci wadanda suke cikin tawagar. Amma wai ba'a basu ko kwandala ba. Yace sun kai su takwas kuma akwai wasu ma da aka basu nera miliyan dari dari wadanda yakamata a tambayesu.
Kwamred Abdulsalami Abubakar jami'in wata kungiya mai rajin yaki da cin hanci da rashawa yace su Yakasai sun dama da sarakuna kuma su sarakunan wasunsu sun yi gagarumar rawa wajen haddasa cin hanci da rashawa a kasar. Yace akwai zargin cewa an ba gwamnoni da sarakuna kudi.
Ga karin bayani.