Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC: Zata gayyato wasu manyan 'yan Najeriya game da badakalar sayen makamai


EFCC
EFCC

A cigaba da binciken yadda aka wawure kudin sayen makamai saboda yaki da Boko Haram hukumar EFCC zata gayyato wasu manyan 'yan kasar akan badakalar

Cikin manyan mutanen da hukumar EFCC zata gayyato sun hada da tsohon shugaban kwamitin amintattun jam'iyyar PDP Chief Tony Anenih da tsohon mai bada shawara ga shugaba Shehu Sahagari Tanko Yakasai da tsohon sakataren gwamnatin tarayya Chief Olu Falae da tsohon gwamnan jihar Oyo Abdulrashid Ladoja.

A firarsa da Muryar Amurka Tanko Yakasai yace abun da ake yi a ksar ya sabawa shari'a.Yace an kama Dasuki amma har zuwa yanzu ba'a shigar da kara akan laifin da ake zarginsa da yi ba.

Akan ko zasu mayar da kudin da aka ce sun karba yace sai sun je kotu tukunna. Yace akwai mutane takwas ko tara da aka baiwa miliyan dari dari amma shi kwamitinsu aka ba kudin.

To saidai a wani halin kuma Kanar Jafaru Isa ya mayarda kashi sittin cikin kudin da aka ce ya karba tare da yin alkawarin biyan sauran nan ba da dadewa ba.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG