Baya ga binciken wadanda ake tuhuma da karkatar da kudi siyan makamai fiye da dala biliyan 2, da kuma sama da dala miliyan 600, hankalin jami’an hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya, EFCC, ya koma kan hukumar hana fasa kwabri wato Kwastam, karkashin tsohon shugaban hukumar Dikko Inde.
Hukumar dai ta kai samame gidan tsohon shugaban hukumar da binciken kwakwab domin gano kudin da suke zargi na haram ne, da neman Dikko Nde, ya dawo Najeriya, daga Daular Larabawa, ko abada sanmacen taso keyarsa gida.
Haka nan baya ga awon gaba da shugaban hukumar bada lasisin gidan Rediyo da talabijin na Najeriya, Emeka Mba, kan zargin badakalar Naira miliyan 15,000, rahotani na nunawa cewa irin wanna bincike zai shiga ofishin tsohon mataimakin shugaban kasa Namadi Sambo.
Kodai dan wanna ya shafi ‘yan tsohowar Gwamnatin PDP, ta Jonathan, wasu ‘yan APC, mai ci a yanzu sun karbi nasu kason da abun har majiyoyi suka tabbatar da bazuwarsa ga sarakunan gargajiya, shugabanin addini harma da ‘yan jarida dasuka amshi kudi don yayata farfagandan ‘yan siyasa da yanzu ake zargi da almundahana.
Wani dan gani kashenin PDP, Faruk Ahmed Gusau, wanda yake babban jami’i, a arewa maso yamma na jami’iyyar yace rabon kudin bai kawo kansu ba.
A nasa bangaren Wazirin Katsina Alhaji Sani Lugga, yana ganin daukar batun siyasa lamarin ko a mutu ko ayi rai bai taso ba in an duba yadda wasu ‘yan siyasa kan yi amfani da bangar ‘yayan talakawa amma da sun haye kujera sais u koma tara abun duniya.
Yana mai cewa “duk rikicin da akayi na siyasa dauki shekara 5, data wuce saboda Allah, kaji a rikicin siyasa an taba kashe Gwamna ko dan Gwamna ko matar Gwamna ko ka taba ji an kashe shugaban kasa ko matar shugaban kasa ko matar shi ko dan uwan shima, duk rikicin da ake na addini ka taba jin wani babban limami an kashe shi, na addini ban cema Bokon Haram ba ko ka taba jin wani babban Reverend an kashe shi, ashe yakamata su na kasa din nan suyi tunani in dai mutun da gaske yake toh ya fito ya yima shugaba ya shiga gaba mu bi shi amma bamu ya tura mu shi ya boye gida ba, in da gaske yake , so yake ya tsare kabilar sat oh ya shiga gaba shi da ‘yayan shi sai mu bi.”