Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Rajin Kare Dimokaradiyya A Nijar Sunyi Watsi Da Kiran Wata Sabuwar Kungiyar Kawance


Ginin majalisar dokokin kasa a Yamai, babban birnin Nijar
Ginin majalisar dokokin kasa a Yamai, babban birnin Nijar

A jamhuriyar Nijar a yayin da ‘yan adawa ke hangen sake kafa wani sabon hadin gwiwa da kungiyoyin fararen hula, domin kalubalantar gwamnati mai ci, sai dai kuma wasu ‘yan rajin kare demokaradiya sun nuna dari dari da wannan shiri a dalilin abinda suka kira alamomin gazawar da ‘yan adawa ke nunawa a gwagwarmayar tabbatar da demokaradiya.

Baban sakataren jam’iyyar MNSD NASSARA Tijjani Abdulkadir, yace sun fara tunanin kafa wata sabuwar hadaka da ‘yan Fararen hula, domin tunkarar gwamnatin shugaba Isuhu Muhammadu, inda yayi kira da duk mutanen da ke son daurewa kan tafarkin dimokaradiya, to ya kasance cikin wannan sabuwar kungiyar hadakar.

Sai dai daga dukkan alamu masu faren hula sun fara dawowa daga rakiyar ‘yan siyasa, alokacin da suke ganin wannan kawance da ake kokarin kullawa ba zai yi wani tasiri ba.

Suma dai shugabannin kawancen kungiyoyin fararen hula na RESISTANCE CITOYEN, dake sukar salon mulkin Isufu Mahamadu cewa su kayi a akai kasuwa.

Daga shekarar 2011 zuwa 2016 kungiyoyin kawance akalla hudu ne jam’iyyun adawa suka kulla da zummar kalubalantar gwamnatin Isuhu Mahamadu.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:43 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG