Baya ga ziyarar da Kwamandan rundunar tsaron kasashen tafkin Chadi Janal Lamidi Adeosun, ya kai Jamhuriyar Nijar a farkon mako, inda har suka tattauna da babban hafsan hafsoshin Nijar Janal Usaini Garba, dangane da halin da ake ciki a yakin da kasashen tafkin Chadi ke yi da kungiyar Boko Haram.
Kwanaki biyu da suka gabata babban hafsan sojojin Najeriya Janal Abayomi Olonisakin, ya ziyarci kasar Nijar inda ya gana da takwaransa na Nijar har na tsawon awa ‘daya da rabi.
Janal Abayomi Olonisakin, ya fadawa manema labara cewa bayan ya tattauna da takwaransa yazo ne ya jinjinawa shugaban kasar saboda goyon bayan da yake baiwa sojojin kasarsa a yakin da ake da Boko Haram, da kuma irin yadda yake bayar da kulawa ga rundunar hadin gwiwa ta yankin tafkin Chadi.
Rikicin Boko Haram wanda ya bazu daga Najeriya zuwa Nijar ta bangaren Kudu maso Gabas, ya haifar da tabarbarewar al’amura da tsayawar harkokin jama’ar yankin.
Domin karin bayani.