Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahukuntan Zambiya Sun Cafke Wasu Mahakun Ma'adinai Mallakar Kasar China


(Foto: Reuters/Marko Đurica)
(Foto: Reuters/Marko Đurica)

Hukumomi a kasar Zambiya sun fada jiya Talata cewa, sun yi ta kokarin tsotse ruwa da laka daga wata ma’adanan tagulla mallakar kasar China inda wasu masu hakar ma’adinai bakwai suka makale a karkashin kasa.

WASHINGTON D. C. - Ma’aikatan ‘yan kasar China biyu da ‘yan kasar Zambiya biyar an kama su ne a ranar Litinin din da ta gabata lokacin da ruwa da laka suka shiga ramin da suke aiki a mahakar ma’adinan Macrolink da ke Ndola mai tazarar kilomita 400 daga babban birnin kasar Lusaka. Daya daga cikin masu hakar ma'adinai ya tsere.

Wasu ‘yan Tanzania masu hakar gwal a Nyarugusu, Geita
Wasu ‘yan Tanzania masu hakar gwal a Nyarugusu, Geita

Jami’in ‘yan sandan lardin Copperbelt Peacewell Mweemba ya shaidawa kamfanin dillacin labarai na Associated Press cewa, hukumomi na tattara kayan aiki daga kamfanonin hakar ma’adinai daban-daban domin abin da suke fatan har yanzu wurin aikin ceto ne.

"A yanzu dai, muna fatan har yanzu suna raye," in ji shi. Kafofin yada labaran cikin gida sun ruwaito cewa, ma’aikatan hakar ma’adinan na aiki ne a kusa da mita 235 (yadi 257) a karkashin kasa.

Kafofin yada labarai na cikin gida sun kuma ruwaito cewa, ma’aikacin hakar ma’adinan da ya tsere, Penjani Kaumba, ya ce ya lura ne da ruwa na fitowa daga wani rami, nan take ya sanar da abokan aikinsa, amma lokaci ya kure.

Zambia na daya daga cikin manyan masu samar da tagulla a duniya, shi ya sa kamfanonin kasar China suka zuba jarin biliyoyin daloli wajen hakar ma'adinai a can.

Wani hatsarin nakiya da aka yi a Zambiya a watan Nuwamba da ta gabata ya kashe mutane akalla 11, yayin da wasu suka bace.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG