Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ghana: Yarjejeniyar Ma’adanin Lithium a Wani Kamfanin Hakar Ma’adinai Na Ostraliya Ya Haifar Da Cece-Kuce


Ma'adinai
Ma'adinai

Kungiyoyin farar hula da wasu masana sun nuna rashin amincewarsu ga sharuddan da aka gindaya a cikin wannan yarjejeniyar, inda suka bukaci gwamnati ta yi gaggawar sake duba yarjejeniyar don tabbatar da kasar ta sami "kaso mafi girma" daga gajiyar albarkatun ma’adinan Lithium din.

A yayin da duniya ke kokarin mayar da hankali wurin amfani da makamashi mara gurbata muhalli, ma’adanin lithium da ake amfani da shi wurin yin batura masu caji, musamman ga motocin lantarki da wasu wayoyin hannu da sauransu, na daga cikin ma’adinai da aka fi yawan bukata a yau, kamar yadda tsohon ministan makamashi na Ghana, John Jinapor ya jaddada, “Sabon tsari yanzu shi ne lithium; Lithium ya fi zinari riba, lithium ya fi lu'u lu'u riba, kuma tsarin duniya yana tafiya zuwa ga wannan koren ma'adini”.

Ma'aikatar filaye da albarkatun kasa a ranar 19 ga Oktoba 2023, ta rattaba hannu kan wata yarjejeniya da kamfanin Barari DV Limited, wani reshen kamfanin Atlantic Lithium Limited na kasar Ostraliya don hakar lithium a garin Ewoyaa da ke karamar hukumar Mfantsiman na yankin Tsakiya.

A wani taron karawa juna sani da Cibiyar Nazarin Harkokin Tattalin Arziki (IEA) ta shirya domin gabatar da sakamakon binciken da masana suka gudanar kan yarjejeniyar ga shugabannin addinai, cibiyar ta bayyana aniyar ta na shigar da kara gaban majalisar dokokin kasar kan yarjejeniyar ma’adanin lithium.

Tsohuwar Alkalin Alkalan Ghana, Mai Shari’a Sophia Akuffo ta gargadi Majalisar da kada ta amince da yarjejeniyar ta Lithium.

Ta ce “Duk abin da IEA ke cewa shi ne, tilas kada majalisa, bai dace ba, ta amince da wannan yarjejeniya da ke hannunmu da aka sanyawa hannu ba. Amma za mu aika da sanarwa ga manema labarai a hukumance”.

Shaikh Armiyau Shuaibu, mai magana da yawun limamin-limamai na Ghana kuma wanda ya wakilce shi a wuri taron, ya bayyanawa Muryar Amurka dalilin da ya sa suka dauki matsayar rashin amincewa da yarjejeniyar.

Ya ce “Duba da yadda aka cutar da mu wajen hako wasu ma’adinai a cikin kasar mu, abin da muke samu bai taka kara ya karya ba. Amma tun da yake wannan sabon ma’adini ne, muna son a yi zurfin tunani da tattaunawa”.

Masana harkokin yau da kullum da kungiyoin farar hula, kamar masanin shari’a Sam Okujeto da masanin tattalin arziki Ransford Gyampo sun fito sun nuna rashin amincewarsu ga yarjejeniyar.

Hamza Attijjany, masanin tattalin arziki yace“Ba mu sami alkalumman yawan adadin abin da za a samu bayan hakar wannan lithium din ba. Idan ba a yi la’akari ba, akwai yiwuwar a yi barnar wannan ma’adani, a karshe amfanin da kasar ta ke ganin za ta samu, ya kasance ba ta samu haka ba”.

Attijjany ya kara muryarsa da cewa, gwamnati ta kara bude kofar tattaunawa kafin ta amince da yarjejeniyar.

Sai dai Ministan filaye da albarkatun kasa, Samuel Abu Jinapor, ya kare yarjejeniyar a wata hira da ya yi da kafar Bloomberg, ya ce yarjejeniyar za ta amfani Ghana, kuma kasar za ta ci gaba da rike mafi girman amfani gwargwadon iko.

Hukumar Makamashi ta Duniya (IEA) ta ce, tsakanin 2017 da 2022, bukatar lithium a duniya ta ninka sau uku, saboda kaura daga man fetur zuwa makamashi mai sabuntawa da za su dace da yanayi.

Saurari rahoton Idris Abdullah:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG