Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Za Ta Yi Hadin Gwiwa Da Bankin Duniya Don Bunkasa Tattalin Arzikin Ma'adinai


Masu hakar ma'adinai
Masu hakar ma'adinai

Gwamnatin tarayyar Najeriya, ta hannun ma’aikatar ma’adinai ta tarayya, cikin wani gaggarumin yunkuri don bunkasa tattalin arziki a Najeriya, za ta yi hadin gwiwa da babban bankin duniya don samun tallafi wajen bunkasawa da karfafa tattalin arziki na ma’adinai a Najeriya.

Sanarwar ta zo ne cikin wata ziyarar ban girma da daraktan bankin duniya a Najeriya Shubham Chaudhuri ya kai wa Ministan ma’adanai na kasa Dele Alake, inda daraktan bankin duniya a Najeriya Shubham Chaudhuri, ya bayyana gamsuwa da yadda gwamnati ta sake mayar da hankali wajen bunkasa albarkatun ma’adanai na kasar.

Masu hakar ma'adinai
Masu hakar ma'adinai

Chaudhuri ya jaddada imaninsa da Najeriya wajen bunkasa fannin ma'adinai ta yadda zai zama babban fanni da zai rinka kawo makudan kudaden shiga wa kasa da kara karfafa daukacin karfin tattalin GDP na kasa idan aka yi da dimbin albarkatun arzikin ma’adinai da ke jibge a Najeriya.

Ya tabbatar da cewa bankin duniya a shirye yake ya yi aiki da ma’aikatar, ba wai kawai don samar da kudade ba, har ma da bayar da tallafin fasaha don inganta ayyukan hakar ma’adinai.

A yayin ziyarar, Alake ya yaba wa bankin duniya bisa rawar da yake takawa wajen ciyar da kasa gaba a sassa daban-daban na tattalin arzikin Najeriya, kuma yana mai yabawa da tallafin da Bankin ya bayar a baya-bayan nan kamar samar da agaji na rage radadi bayan cire tallafin man fetur da tallafe tallafe da dama da banki duniya ke bayarwa ma Najeriya.

Dele Alake
Dele Alake

Alake ya bayyana kyakkyawan fata game da ƙarfafa haɗin gwiwa don samar da kudade masu mahimmanci ga muhimman wurare a fannin hakar ma'adinai masu mahimmancin gaske ga kasa.

Ministan ya bayyana shirin ma’aikatar ma’adinai ta kasa wajen sanya hannun jari a bangaren bincike don tattara muhimman bayanan kasa da za su taimaka wa masu zuba jari a fannin ma’adinai wajen yanke shawara. Ya kuma yi magana game da ci gaba da kokarin samar da ingantattun tsare-tsare na gwamnati da kuma kiyaye muhalli cikin harkokin hakar ma’adinai a kasa.

Alake ya tabbatar da kudurin Gwamnatin Tarayya na samar da yanayi mai kyau na ayyukan hakar ma’adanai, inda ya bayyana alfanun da za a samu ga al’umma da kuma kudaden shiga ta hanyar biyan haraji.

"Na gode muku da kuka shiga cikin aikin 'min diver', duk da cewa shirin ya rigada ya zo ƙarshe. Zamu cigaba da karfafa haɗin gwiwarmu wajen samar da kudade ga muhimman abubuwan da zasu kara karfafa tattalin arzikin ma'adinai, kuma muna kyautata zaton samun tallafi daga gareku musamman a fannoni da suke da bukatar ilimin fasahar zamani,” in ji Alake.

Tawagar Bankin Duniya, da suka hada da Daraktan Kasa Shubham Chaudhuri da Jagoran Shirye-shiryen Bertina Kamphuis, sun kara tattaunawa kan sharudda da suka dace don aiwatar da ayyuka masu inganci a Najeriya.

Mai sharhi kan tattalin arziki na yau da kullum, Yusha’u Aliyu yayi wa Muryar Amurka karin haske a Abuja inda yace

“Nasarar irin wadannan yarjejeniyoyi da akayi tsakanin gwamnatoci da hukumomin duniya musamman babban bankin duniya, ta ta’allaka ne da irin tsare-tsare masu ma’ana da gwamnati ta shimfida, wanda hakan tamkar kira ne ga masu zuba hanun jari da ‘yan kasuwa wajen kara imani da kuma zuba hanun jari a kasa don bunkasa tattalin arziki.

A yanzu tattalin arzikin Najeriya ya dogara ne kaco-kan ga danyan man fetur da ake hakowa, indai ana so a bunkasa wasu bangarorin ma’adinai da ke jibge a kasa to dole ne gwamnati ta samar da yanayi mai kyau da zai karfafa masu zuba jari da kuma tsare-tsare masu inganci, domin yanzu haka kusan babu wata jiha a Najeriya da ba ta da wani ma’adinan arzikin kasa wanda da za’a maida hankali a kai to tabbas za’a samu arziki mai yawa”

Bugu da kari, Malam Aliyu ya kara da cewa, ba samun kudin bane matsalar a Najeriya said ai in har hakan zai tabbata to dole gwamnati sai ta tabbatar da samar da tsaro da yanayi mai kyau da kare muhalli, misali kamar a garin Jos a baya anyi ta hakar ma’adinai da dama inda akai ta haka ramuka amma wadannan ramuka da aka haka har yanzu suna nan kuma sun cin rayukan mutane da dabbobi, don haka duk yarjejeniyar da za a shigar dole ne ayi la’akari da irin wadannan abubuwa da fitar da tsare-tsare don magance irin wadannan matsaloli tare da kauce masu.

Malam Yusha’u ya kara da cewa “yana da kyau cikin wannan hadin gwiwa ya zama cewa babban bankin duniya ya sanya kare muhalli, rayuka da dabbobi ciki, kare hakkin masu zuba hannun jari harma da kare muraden kasar wajen bunkasar tattalin arzikinta”

Kokarin hadin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da Bankin Duniya na habaka fannin hakar ma’adanai na nuni da wani muhimmin mataki na bunkasar tattalin arziki mai dorewa a Najeriya.

Imani da minista Alake yayi game da rawar da bankin duniya ke takawa a tarihi, tare da nuna kwarin gwiwar yin hadin gwiwa a nan gaba, ya nuna muhimmancin hadin gwiwa tsakanin kasa da manyan hukumomi na duniya wajen samar da ci gaba mai ma'ana, yayin da bangaren ma'adinai ke taka muhimmiyar rawa wajen samar da tattalin arzikin kasa, zuba jari a fannin bincike na fasahar zamani na da matukar muhimmanci, kuma samun tallafi daga bankin duniya a irin wadanan fannoni babu shakka zai taimaka wa Najeriya matuka musamman lura da cigaban fasahar zamani da ake samu yanzu a duniya.

~ Yusuf Aminu Yusuf

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG