Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taraba: An Kama Masu Hakar Ma’adinai 3,500, Biyu Sun Mutu


Masu hakar ma'adinai da aka kama a Taraba
Masu hakar ma'adinai da aka kama a Taraba

Ana ci gaba da rigingimu kan harkokin hakar ma'adinai a fadin Najeriya. A baya bayan nan al'amarin na kara muni a arewacin Najeriya. Wannan karon an kama dubban wadanda ake zargi da hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba a jihar Taraba.

Jami’an Kwamitin Aiki Da Cikawa (Task Force) na hadin gwiwa da Gwamnatin jihar Taraba ta kafa don gyara sana’ar hakar ma’adanai a jihar, sun kama wasu mutane dubu uku da dari biyar (3,500) da ake zargi da hakar ma’adanai ba bisa ka’ida ba. Wani daga cikin wadanda ya gaya ma wakilin Muryar Amurka cewa an kashe biyu daga cikinsu.

Wadanda aka Kaman na ikirarin cewa inda aka kama su ba ya cikin jihar Taraba; ya na cikin Karamar Hukumar Tongo ne a jihar Adamawa. Su na ikirarin cewa suna da takardun hakar ma’adinan, don haka ba su saba wata doka ba. Hasali ma, daya daga cikin wadanda aka kama din, Malam Ayuba Aminu Buba, na zargin cewa dukiyarsa na miliyoyin naira, ciki har da tsabar kudi wajen miliyan daya da dari hudu, sun salwanta a wannan samamen da jami’an aiki da cikawan su ka kai.

To sai dai shugaban Kwamitin Aiki da cikawan, Janar Burgediya Jeremiah Aliyu Faransa (murabus) ya karyata cewa a jihar Adamawa su ka yi kamen. Ya ce a jihar Taraba su ka kama masu hakar ma’adinan ba a jihar Adamawa kamar yadda wadanda aka Kaman su ke ikirari ba. Ya kuma karyata zargin cewa jami’an kwamitin sun karkashe wasu daga cikin masu hakar ma’adinan.

Saurari rahoton Muhd Lado Salisu Garba:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:43 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG