Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

China Na Fadada Huldar Ta A Kasashen Africa


China da wasu shugabanin Afirka
China da wasu shugabanin Afirka

Yayinda hukumomin mulkin soja a Nijar ke raba gari da kasashen yamma, kasar China na amfani da wannnan damar wajen kulla yarjejeniyoyi daban daban da sojojin kasar.

Kanfanin kasar China zai soma aikin hako Uranuim à arewacin kasar, lamarin da zai sanya Nijar ta zama kasa ta uku mafi ma'adinan uranuim a duniya.

Sai dai kungiyoyi gwagwarmaya à Nijar sun bukaci jagororin kasar su soke duk wani lasisi na hako ma'adinan Uranuim a cikin kasar duba da yadda aka shafe shekaru kusan 50 ana fitar dashi amma kuma Nijar bata anfana da komai ba.

Masu hakar ma'adinai
Masu hakar ma'adinai

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin mulkin sojojin Nijar karkashin jagorancin Abdurahmane Tchaini suka raba gari da kasashen yamma musan man Faransa da ta yi wa Nijar mulkin mallaka.

Ana dai kallon wannan yunkurin na kasar China na kyautata dangantaka da jagororin mulkin sojan kasar ta Nijar domin karfafa tasirin ta a kasar ta Nijar.

kamfanin COMINAK
kamfanin COMINAK

Nijar dai tana daga cikin kasashen dake fuskantar matsalar gurbata muhalli inda yake haifarwa kasar ambaliyar ruwa da kwararowar hamada da kuma takaituwar filayen noma da kiwo to sai dai kungiyoyin kare muhalli na gargadi dangane da gurbata muhalli daga aikin hako ma’adinai da kanfanonin ke aikatawa inda suka yi kira ga hukumomi da su sanya ido akan kanfanonin.

Saurari rahoton Hamid Mahmud:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:01 0:00

Dandalin Mu Tattauna

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG