Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru: Hukumomi Sun Kafa Dokar Rufe Wuraren Hakar Zinari


Wurin Hakar Zinari a Kasar Kamaru
Wurin Hakar Zinari a Kasar Kamaru

Hukumomin kasar Kamaru sun yanke shawarar rufe mu'adinan zinari bayan an samu asarar rayuka da dama a ma'adinan zinare da ke yankin Gabas, wuraren.

Kamfanonin hakar ma'adinai da aka dakatar sun hada da wadanda da ke aiki a wasu kananan masana'antu na zinare a wurin hakar ma'adinai na Kambelé III, wani yanki kusa da gundumar Batouri a yankin Gabas.

Hakimin Kadey, Djadaï Yakouba, ya sanya hannu a kan wata doka a ranar Laraba 27 ga Yuli, 2022, inda ya sanar da rufe su. "Dukkan kamfanonin hakar ma'adinai da ke aiki a Kambelé, an rufe su daga ranar da aka sanya hannu kan wannan doka har zuwa wani sanarwa," in ji shi.

Dokar ta samu karbuwa a wurin kungiyoyin fararen hula kamar yadda Dr Samuel Guifo magatakardar wata kungiyar yace

"Mun yi farin cikin da wannan dokar, ko da yake mun so a dau wannan dokar tun ba’a samu mace mace da yawa ba "

Ya kara da cewa "Albarkacin wannan dokar, za mu ci gaba da taimakawa iyalan ma’ikata da suka rasa rayukansu ko suka jikkata a gaban hukuma a sanadiyar wannan aiki"

Wannan dokar ta samo asali ne daga mace-mace da aka samu a wannan wurin hakar ma'adinai. Haƙiƙa shugaban wannan sashe ya nuna rashin jin dadn sake faruwar mace-macen da suka faru ta hanyar nutsewar ruwa sakamakon rashin rufe ramukan ma’adanai; yawan mutuwar mutane ta hanyar zaftarewar kasa saboda rashin bin ka'idojin ma'adinai; da kuma barazanar lalacewar titin kasa mai lamba 10.

A nashi bayanin, Martial Ngadji shugaban kungiyar ma’zauna Kambélé III ya ce, rashin kayan aiki irin na zamani na daga cikin abuwan da suke kawo wannan matsala. Yan kasar Sin da suke nan basu damu da kiyaye tsare rayukan mutane ba, su dai su hako ma’adinai ne kawai nasu.

Ana zargin kamfanonin da ke aiki a wannan yanki da karkatar da kasa ko wace rana ta hanyar tono shebur, da yin watsi da su. Wannan yana haifar da tafkunan wucin gadi waɗanda ke cutar da muhalli. A cikin Satumba 2021, hukumar farar hula mai suna Forests and Rural Development (Foder) ta gano ramuka 703 da aka yi watsi da su, ciki har da tafkunan wucin gadi 139 a wani yanki. Hakika, masu aikin hakar ma'adinai suna fuskantar haɗari mai tsanani a duk tsawon yini, kuma rahotanni kaɗan ne suka yi gargaɗi game da irin haɗarin da ke tattare da su.

Idan dai ba a manta ba, daga shekarar 2014 zuwa watan Yunin 2022, kungiyar Foder ta bada rahoton mutuwar mutane 199 da kuma munanan hadurruka sama da 133 da suka afku a wurare daban-daban na hakar gwal a yankunan gabashi da kuma Adamaoua.

Saurari cikakken rahoton Mohamed Ladan cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

XS
SM
MD
LG