Kotun ta kuma ci tarar sidi GH¢48,000 kwatankwashin dalar Amurka dubu hudu.
An zargi Aisha Huang da kasancewa daya daga cikin masu hannu dumu dumu wajen gurbata muhalli sakamakon hakar gwal ba bisa kaida ba, musamman a yankin Ashanti.
Tun da farko an kama ta tare da tasa keyarta zuwa kasarta ta asali a shekarar 2018, bayan da babban mai shigar da karar ta gwamnati ya yanke shawarar dakatar da shari’ar da ake yi mata inda ake zarginta da aikata laifukan hakar ma'adinai ba bisa kaida ba.
Sai dai kuma rahotanni sun nuna cewa, ta sake shiga kasar ne domin ta ci gaba da wannan sana'ar da tayi sanadin korarta daga kasar.
A watan Oktoban 2022, Atoni janar din kasar ya yanke shawarar gurfanar da ita a gaban kotu bisa laifin da ake zarginta da shi kafin a kore ta da kuma wasu da ta aikata tun shigowarta kasar.
A cikin tuhumar na baya bayannan, masu shigar da kara sun ce Aisha ta samu izinin hakar ma’adinan ba bisa ka’ida ba, a wani gari mai suna Bepotenten da ke gundumar Amansie ta Yamma a yankin Ashanti, sannan kuma tana gudanar da wani kamfani mai tallafawa masu hakar ma’adinai, tare da daukan 'yan kasashen waje aiki ba bisa kaida ba, dama shiga kasar bayan an haramta mata hakan.
Aisha Huang ta musanta aikata wadannan laifuka kuma lauyoyinta sun bukaci da a tasa keyarta zuwa China maimakon daure ta a gidan kaso, sai dai Alkalin kotun bai amince da hakan ba.
Bayan zantar da hukunci mataimakin atoni janar din kasar ya fadawa manema labaru cewa, ba wannan kadai ne karar da ya shigar na masu hakar ma'adinai ba bisa kaida ba, kuma zasu cigaba da hakan har sai an kawo karshen wannan kazamin aiki.
Rahotonni na baya-bayan nan da hukumar kula da gandun dazuka ta Ghana ta fitar sun nuna cewa, Ghana ta yi asarar gandun dazuka kusan hekta 5000 a cikin dazuka 34 saboda hakar ma'adinai ba bisa ka'ida ba. Matsalan da ke barazana ga rayuka dabbobi da ruwan sha da gonaki dade sauransu.
Tun shekarar 1989 da gwamnatin Ghana ta samar da dokar hakar ma’adinai a kananan filaye, kasar bata fuskanci matsala mai girma na gurbatar muhalli ba, sai dia wadansu 'yan kasashen waje musamman 'yan kasar China, suna shiga sana’ar ta barauniyar hanyar, abinda ya janyo mummunan tasiri ga muhalli tare da tattalin arzikin kasar.
Saurari rahoton Hamza Adams:
Dandalin Mu Tattauna