Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

"Kawayen Siriya" na bukatar a bari a shigar da kayan agaji kwanan nan


Barin wuta a birnin Homs na Siriya
Barin wuta a birnin Homs na Siriya

Wani rukunin kasashen Yamma da na Larabawa da ke taro a kasar Tunisiya

Wani rukunin kasashen Yamma da na Larabawa da ke taro a kasar Tunisiya, na shirin gabatar da bukatar hukumomin Syria ko Sham, su dau alkawarin kawo karshen dukkannin nau’ukan tashe-tashen hankula ba tare da bata lokaci ba, su kuma bari a shigo da kayan agaji zuwa wuraren da ke matukar fama, cikin ‘yan kwanaki kadan.

A wani daftarin shela da ake shirin gabatarwa a taron wadanda ake kira “Kawayen Syria,” ana sa ran jami’an diflomasiyya za su yi kira ga Shugaban Syria Bashar al-Assad da ya bayar da umurnin tsaida murkushe zanga-zangar da aka yi watanni 11 ana yi, saboda a iya kai kayan agajin cikin awoyi 48.

Mazauna birnin Homs na yankin tsakiyar Syria, sun ce akwai tsananin karancin abinci da ruwa da magunguna, bayan barin wutar da dakarun da ke biyayya ga Assad su ka yi na tsawon sata 3, bayan sun yi wa wannan gari na ‘yan tawaye kawanya.

Wakilai daga kasashe sama da 70 da kungiyoyin kasa da kasa ne ke halartar wannan taron, cikinsu har da Sakatariyar Harkokin Wajen Amurka Hillary Clinton. Da kasar Rasha da China sun ce ba za su taron na Tunisiya ba. Kasashen biyu sun sha yin kafar ungulu wa kudurin kwamitin tsaron MDD na daukar mataki kan Syria, da cewa bai kamata kwamitin ya yi katsalanda cikin harkokin cikin gidan Syria ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG