Hukumomin kasar Sin wato China sun ce mutane fiye da miliyan uku na kara rasa ruwan sha a lardin Yunnan, a daidai lokacin da wani bala’in farin shekara uku ke ci gaba da yin illa ga rayuwar mutane da ta dabbobi da kuma sha’anin noma a lardin na kudu maso yammacin kasar.
Kafofin yada labaran gwamnatin kasar China sun ruwaito hukumomin lardin Yunnan su na cewa wani daji mai fadin kadada sama da dubu dari da talati, na fuskantar karuwar barazanar wutar daji a daidai lokacin da albarkatun noma su ka yankwane a wasu gonakin da fadin su ya wuce kadada dubu dari biyar.
Wani gidan talbijin ya nuna kwaryar kogin Xihe a kekashe a karamar hukumar Weishan. An ruwaito mazauna yankin su na cewa kimanin sulusi biyu, wato kashi biyu cikin uku, na manoman wani kauye gaba daya sun sayar da dabbobin su masu dimbin yawa saboda rashin ruwan shayar da su.
Jami’an hukumar ceton masu fama da bala’in farin sun ce wasu kananan tankunan ruwa su kimanin dari hudu da ke yankin, na nan yanzu haka babu ruwa a cikin su, sannan kuma su ka ce wasu koguna, matsakaita da kanana-kanana, su kimanin dari biyu da hamsin na ci gaba da kafewa.