Jiya laraba Jami’an Gwamnatin Korea ta Arewa suka sanya hannu kan wani daftarin yarjejeniyar dakatar da gwaje-gwajen makaman nukiliya na gajeren lokaci, sannan a dakatar da tacewar da ake yiwa sanadaran Uranium dake taimakawa a kai ga kera makamin Nukiliya.
An cimma wannan yarjejeniyar ne tare da jami’an Amurka bayan wata tattaunawar fahimtar juna dac aka yi tsakanin jami’an Korea ta Arewa da na Amurka a birnin Being na China.
An kuma sami nasarar cimma dai daituwar haka ne watanni biyu da rasuwar shugaba kuma jagoran ‘yan kwamanist na Korea ta Arewa Kim Jong II.
A nan birnin Washington kuma, fadar shugaban Amurka ta White House ta yaba da cimma wannan daidaituwa. Sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta shaidawa kwamatin majalisar dokokin Amurka jiya laraba cewar Korea ta Arewa ta yarda ta jingine wasu abubuwan da suka danganci makaman nukiliya domin a saka mata da isassun kayan abinchi.