Yau Lahadi ake zaben shugaban kasa a bangarorin gabashin kasar Rasha, zaben da kila ya sake maida Vladimir Putin kan ragamar mulki a karo na uku na wani wa’adin shekaru shidda da zai shiga tarihi.
A yayinda aka fara zaben ne masu aikin sa kai dubu maitan suka fara nazarin zaben tare da fatar zasu rage yawan magudi irin wadda ta faru a zaben Majalisar dokoki da aka yi a ranar hudu ga watan disamban bara.
Wasu masu aikin sa kai dubu dari shidda kuma, wadanda ke amfani da kwaputa, suma sunyi rajista domin nazarin kamararorin da aka kakkafa a kusan dukkan rumfunan zaben kasar dubu dari.
Kafin dai zaben na yau, masu hamaiya sunyi zanga zangar a duk fadin kasar domin nunawa Mr Putin da jam’iyarsa ta United Rasha wadda take jan ragamar mulki rashin amincewa. Haka kuma Mr Putin ya fuskanci zanga zanga a wuraren daya je yakin neman zabe.
Tun dai lokacinda jam’yar Mr Putin ta United Rasha ta lashe zaben Majalisar dokoki da aka yi a watan disamba, dubban yan kasar suka fito tituna suna zanga zanga. Masu zanga zanga sunyi ikirarin cewa jam’iyar ta lashe zaben ne ta hanyar yin magudin cika akwatuna da kuri’un karya, zarge zargen da jam’iyar United Rasha ta musunta.
Kididdiga da aka yi a kwanan nan sun nuna cewa kashi tamanin daga cikin dari na yan Rasha sunyi imanin cewa Mr Putin zai sake darewa kan ragamar mulki, a yayinda kashi hamsin da bakwai daga cikin dari kuma suka yi imanin cewa har yanzu shine shugaban kasa, duk da cewa a hukunce Dmitry Medvedev shine shugaban kasar.
Idan dai ba’a mance ba, Mr Putin yayi wa’din mulki har sau biyu daga shekara ta dubu biyu zuwa shekara ta dubu biyu da takwas kafin ya zama Prime Minista.