Shugaban kasar Sham, wanda ya kasa jin sakat a saboda fitina a kasarsa, yayi alkawarin goyon bayan abinda ya kira “duk wani yunkuri na tsakani da Allah” na kawo zaman lafiya a kasarsa.
Kafofin yada labarai na kasar ta Sham sun ce shugaba Bashar al-Assad yayi wannan furucin a bayan ganawar da yayi yau asabar da tsohon babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya, Kofi Annan, a birnin Damascus. Har ila yau, shugaba Assad yayi gargadin cewa babu yadda za a iya samun sasantawar siyasa mudiin aka kyale ‘yan ta’adda su na ci gaba da haddasa yamutsi a kan titunan kasar.
Wannan furuci na shugaban Sham yana zuwa a daidai lokacin da dakarun gwamnati suke ci gaba da kai farmaki a kan birnin Idlib na arewa maso yammacin kasar.
Mr. Annan, wanda shi ne sabon wakilin Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasashen Larabawa kan batun kasar Sham, yayi kiran da a warware wannan rikici ta hanyar sulhu, yana mai gargadin cewa yunkurin da wasu ke yi na samar da makamai ga sojojin ‘yan tawaye zai kara munin lamarin ne kawai. An shirya Mr. Annan zai gana da fararen hular kasar ta Sham kafin ya bar Damascus.
Masarautar Qatar, daya daga cikin kasashen dake cikin kungiyar kasashen larabawa, ta fadawa wani taron ministocin harkokin wajen larabawa yau asabar a birnin al-Qahira cewa lokaci yayi na tura sojojin kasashen larabawa da na waje zuwa kasar Sham mai fama da fitina.
Shi ma ministan harkokin wajen Rasha, Sergei Lavrov, ya halarci taron da aka yi a Misra. Sau biyu kasar Rasha da China su na hawa kujerar naki domin shure kudurorin da aka so gabatarwa a gaban Kwamitin Sulhun MDD da nufin kara matsin lamba a kan gwamnatin shugaba Assad don kawo karshen wannan rikicin.