Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rasha da China sun hau kujerar naki kan batun kasar Siriya


Wani zaman kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya
Wani zaman kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya

Al'ummomin kasashen duniya sun bayyana takaicin hawa kujerar naki da kasashen Rasha da China suka yi kan rikicin siriya.

Hawa kujerar naki da kasashen Rasha da China suka yi a kan kudurin kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya dangane da Siriya da ya yi Allah wadai da murkushe mutanenshi da shugaba Bashar al-Assad, yake yi da kuma kira gare shi da ya sauka daga karagar mulki ya harzuka jama’a a duk fadin duniya.

Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-moon ya kushewa gaza amincewa da kudurin, da cewa, kwamitin sulhun ya yi rashin damar daukar matakin bai daya da zai taimaka wajen shawo kan rikicin. Sauran membobin kwamitin sulhun goma sha uku , da suka hada da Amurka da Faransa da kuma Jamus sun amince da daftarin.

Firai Ministan kasar Tunisiya ya bayyana yau Lahadi cewa kasarshi zata yanke hulda da Siriya. Hamadi Jebali yace Tunisiya zata kori jakaden kasar Siriya daga kasar, ta kuma yi kira ga sauran kasashen larabawa su bi sahunta.

Bayan kada kuri’ar jiya asabar jakadiyar Amurka Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice tace Washington tayi allah wadai da hawa kujerar nakid a Rasha da kuma China suka yi. Sai dai tace Amurka ba zata karaya ba game da batun kasar Siriya.

Jakaden Birtaniya a Majalisar Dinkin Duniya Mark Lyall Granta yace Rasha da China sun juyawa kasashen larabawa baya ta wajen goyon bayan mulkin kama karya.

Jakaden kasar Siriya a Majalisar Dinkin Duniya Bashar Ja’afari ya zargi membobin Majalisar Dinkin Duniya da goyon bayan wadanda ya kira” ‘yan ta’adda dake dauke da makamai” .

XS
SM
MD
LG