Baban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Banki Moon, yayi kira ga kasar Syria data yiwa Allah ta bar ma’aikatan agaji na jin kai su samu sukunin kaiwa ga mutane da suke bukatar taimako ruwa a jallo, a yankunan data yiwa kawanya.
Jiya juma’a Mr Banki Moon yace Majalisar Dinkin Duniya tana ci gaba da samu rahotani yadda ake karkashewa da tsarewa babu gaira babu dalili da kuma yadda ake galazawa jama’a. Baban sakataren yayi wannan furucin ne bayan da kungiyar gaji da Red Cross tace hukumomin Syria sun hana ma’aikatanta, jigilar magunguna da sauran kayayyakin agaji a unguwar Baba Amir a birnin Homs da yaki ya daidaita.
Shugaban kwamitin kungiyar Red Cross Jakob Kellenberger yace an hana jerin gwanon manyan motoci guda bakwai wadanda ke jigilar kayayyakin agaji shiga unguwar Baba Amr inda yau kusan wata guda ke nan da sojojin gwamnati suka kilace mazauna birnin da yan tawaye. Kwamitin kungiyar Red Cross yace da farko gwamnati ta basu izini a ranar Alhamis cewa su shiga anguwar.
Mr Kellenberger ya tabbatar cewa ma’aikatansa dana takwaran kungiyar Red Cross a Syria zasu kwana a Homs tare da fatar gwamnatin Syria zata bari suyi jigilar kayayyakin agaji zuwa unguwar Baba Amr nan bada jimawa ba.