‘Yan gwaggwamaya a Misira suna shirin gudanar da wani yajin aiki na wuni guda domin bukin cika shekara guda da hambare gwamnatin shugaba Hosni Mubarak.
Wannan sabon matakin ya biyi bayan zanga zanga da dama da aka yi ta kira ga shugabannin mulkin sojan kasar su mika mulki.
Majalisar Koli ta rundunar soji wadda ta karbi ragamar shugabanci, bayanda Murabark ya mika mulki a watan Fabrairu da ta gabata, tace barazana da matsin lamba ba zasu sa ta gaggauta mika mulki ga farin kaya ba.
Jiya jumma’a, dubban Misirawa suka yi jerin gwano zuwa ma’aikatar tsaro dake Alkahira babban birnin kasar.
Shugabannin mulkin soja sun yi alkawarin gudanar da zaben shugaban kasa a watan Yuni wanda zai kasance cika makin shirin mika mulki ga farin kaya.
Rundunar sojin dake mulki ta kuma gudanar da zaben majalisa da aka gudanar rukuni rukuni da ya kai ga kafa sabuwar majalisa da jam’iyun ‘yan kishin Islama suka mamaye.