Kungiyar hadin kan Larabawa ta bayyana amincewa da murabus din hafsan sojin kasar Sudan wanda ya jagoranci tawagar sa ido ta kungiyar da tayi aiki a Siriya, kuma zata zabi tsohon ministan harkokin kasashen ketare na Jordan a matsayin sabon manzon kungiyar mai sa ido a rikicin kasar Siriya.
Jami’ai sun ce Janar Mohammed Ahmed al-Dabi ya ajiya aiki ne yau lahadi, yayinda ministocin kasashen ketare na kungiyar da ta kunshi kasashe 22 suke taro a birnin alkahira, domin tattauna a kan sabon matakin hadin guiwa tsakanin kungiyar hadin kan Labarawa da Majalisar Dinkin Duniya da zasu dauka a Siriya.
Sabuwar tawagar sa idon zata maye gurbin wadda aka janye watan jiya bayan da aka sami karin tashin hankali a Siriya. Jami’an kungiyar sun ce an tura Cif Nabil Elaraby ya tuntubi Abdel Elah al-Khatib da nufin nemanshi ya maye gurbin al-Dabi. Al-Khatib shine tsohon manzon Majalisar Dinkin Duniya a Libya.
Kasashen Larabawan dake mashigin tekun Gulf sun janye masu sa idonsu ne domin nuna fushinsu da yadda gwamnatin kasar Siriya ta ki daina murkushe zanga zangar da ake gudanarwa na tsawon watanni goma sha daya.
Ana kyautata zaton ministocin kungiyar hadin kan Labarawan zasu tattaunawa kan yiwuwar amincewa da kungiyar Majalisar hadin kan kasar Siriya dake Istanbul a matsayin mai wakiltar kungiyoyin hamayyar kasar
Majalisar Dinkin Duniya tayi kiyasin cewa adadin wadanda ake danganta mutuwarsu da tashin hankalin ya haura dubu biyar da dari hudu. Sai dai watan jiya cibiyar ta duniya ta bayyana cewa ta daina tara adadin mamatan domin samun bayanai yana da wuya ainun