Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Kasashen Yammacin Afirka Suna Barazanar Amfani Da karfin Soja A Ivory Coast.


Daga hanun dama,shugaba Goodluck Jonathan na najeriya yake tattaunawa dashugaban jamhuriyar Benin yayi Boni,a lokacin taron gaggawar kungiyar ECOWAS a Abuja ranar jumma'a.
Daga hanun dama,shugaba Goodluck Jonathan na najeriya yake tattaunawa dashugaban jamhuriyar Benin yayi Boni,a lokacin taron gaggawar kungiyar ECOWAS a Abuja ranar jumma'a.

Shugabannin kasashe dake yammacin Afirka suna barazanar amfani da karfin soja su tilastawa shugaba Laurent Gbagbo ya bar mulki, idan bai yarda da sakamakon zaben kasar ya mika mulki cikin lumana ba.

Shugabannin kasashe dake yammacin Afirka suna barazanar amfani da karfin soja su tilastawa shugaba Laurent Gbagbo ya bar mulki,idan bai yarda da sakamakon zaben kasar ya mika mulki cikin lumana ba.

Jiya Jumma’a ce shugabannin kasashen suka tsai da wan nan shawarara a Najeriya bayan wani taro da suka yi,sun ce zasu tura wata tawaga mai karfin gaske zuwa Cote D’voire, da nufin shawo kan Mr.Gbagbo ya mika mulki cikin ruwan sanyi.

Suka ce idan ya ki,kasashe makwabta zasu da wani zabi illa daukan wasu matakai da zasu hada da karfin soja,wajen ganin an mutunta sakamakon zaben.

Kungiyar Tarayyar Afirka,MDD,da wasu kasashe dadama sun yi na’am da zaben Alassane Ouattara a zaben da aka yi cikin watan Nuwamba. Tun lokacin Mr. Gbagbo ya ki saurarawa duk kiraye kiraye da aka masa na sauka daga mulki.

Majalisar Dinkin Duniya, tace an kashe fiyeda mutane 170 a tarozma da ta biyo bayan zaben. Sojoji masu biyayya ga Mr. Gbago da wasu ‘yan banga da suka rufe fuskokinsu sun hana zuwa wani wuri da ake zargin abinne gawarwakinmutane masu yawa a kauyen N’Dotre.

XS
SM
MD
LG