Kungiyar Tarayyar Turai ta ce zata kafa takunkumi a kan shugaba Laurent Gbagbo na kasar Ivory Coast, wanda ya ki sauka daga kan mulki a bayan zaben watan da ya shige. Wata mai magana da yawun Kungiyar Tarayyar Turai ta fada yau litinin cewa Mr. Gbagbo da matarsa su na cikin ‘yan Ivory Coast goma sha tara da za a kafawa takunkumin. Mr. gbagbo ya ki yarda ya mika mulki ga Alassane Ouattara, mutumin da duniya ta amince a zaman wanda ya lashe zaben na shugaban kasa. A yayin da wannan gardamar siyasa ke ci gaba da ruruwa, Majalisar Dinkin Duniya ta bada rahoton kashe-kashe da sace mutane dake wakana a kasar Ivory Coast. Babbar kwamishinar kula da kare hakkin bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya, Navi Pillay, ta bayar da sanarwa jiya lahadi, inda take cewa an kashe mutane fiye da hamsin, yayin da wasu fiye da dari biyu sun ji rauni kama daga ranar alhamis. Pillay ta ce ana samun karin shaidar dake nuna cewa ana mummunar keta hakkin bil Adama a kasar Ivory Coast. Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a kasar yace ya samu daruruwan rahotanni na wasu ‘yan bindiga cikin rigunan soja su na sace mutane daga cikin gidajensu.
Kungiyar Tarayyar Turai ta ce zata kafa takunkumi a kan shugaba Laurent Gbagbo na kasar Ivory Coast.
Kungiyar Tarayyar Turai ta ce zata kafa takunkumi a kan shugaba Laurent Gbagbo na kasar Ivory Coast, wanda ya ki sauka daga kan mulki a bayan zaben watan da ya shige