Babban bankin Afirka ta Yamma ya tsinke hanyoyin da Laurent Gbagbo zai bi ya karba ko ya taba kudaden Ivory Coast, ya kuma bayyana amincewa da Alassane Ouattara a zaman shugaban kasar na halal.
Ana sa ran cewa wannan mataki da bankin ya dauka zai kara matsin lamba a kan Mr. Gbagbo da ya sauka daga kan mulki, tare da jefa shi cikin wahalar yadda zai yi ya samo kudaden da zai biya albashin ma'aikatan gwamnati da sojoji masu yi masa biyayya.
Jiya alhamis, an tsinke nuna tashar telebijin ta gwamnati dake hannun Mr. Gbagbo a birane da dama dake wajen Abidjan.
Su kuma shugabannin Afirka ta Yamma, su na yin taron gaggawa yau Jumma'a a Abuja, babban birnin Najeriya, a kan hanyar da ta fi dacewa ta takalar rikicin dake karuwa a kasar Ivory Coast.
Wannan shi ne karo na biyu da Kungiyar Tarayyar Afirka ta Yamma, ECOWAS ko CDEAO, mai wakilai 15, ta ke taron kolin gaggawa tun bayan zaben shugaban kasa watan da ya shige a Ivory Coast.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce an kashe mutane akalla 173 a cikin mako gudan da ya biyo bayan kiyawar Mr. Gbagbo da ya sauka daga kan karagar mulki.