Faransa ta shawarci ‘yan kasarta das u fice daga kasar ivory Coast, a daidai lokacinda babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban ki-Moon yake kashedin cewa kasar ta Cote d’Ivoire na fuskantar barazanar abkawa cikin wani sabon yakin basasa gadangadan. Akwai faransawa kamar dubu 15 a kasar ta Ivory Coast, wanda yassa gwamnatin Faransan ke gaya musu cewa, in zasu iya, su barta, su koma wata kasar, su yi zaman wucingadi na wani dan lokaci. Har yanzu hinjararren shugaban Cote d’Ivoire din, Laurent Gbagbo yana ci gaba da nacewa akan cewa shine shugaban kasar day a lashe zaben da ake takkada a kansa da akayi na shugaban kasa a watan Nuwamban day a gabata, wanda amma kuma duk duniya ta dauka cewa Alassane Ouattara ne ya lashes hi. A jawabin da yayi jiya inda yake dada jadadda cewa har yanzu ragamar mulkin kjasar na hannunshi, Gbagbo yace baya son ganin jinni ya malala. Yace yana gayyatar wakilan Kungiyar Tarayyar Turai, Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Tarayyar Turai su zo su zauna, su sake nazarin sakamakon zaben.
Faransa ta shawarci ‘yan kasarta das u fice daga kasar ivory Coast