Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Afirka Uku Na Shirin Ganawa Da Gbagbo


Sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin Duniya a Abidjan,inda shugabannin kasasehn dake ECOWAS suka yada zango na farko a kasar.
Sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar dinkin Duniya a Abidjan,inda shugabannin kasasehn dake ECOWAS suka yada zango na farko a kasar.

Wata tawaggar shugabannin kasashen Afrika na haramar fuskantar bijirarren shugaban Ivory Coast Laurent Gbagbo da bashi zabin ya sauka daga kan karagar mulki ta hanyar aminta da cewa ya sha kaye a zaben shugaban kasan da aka yi a watan jiya.

Wata tawaggar shugabannin kasashen Afrika na haramar fuskantar bijirarren shugaban ivory Coast Laurent Gbagbo, da bashi zabin ya sauka daga kan karagar mulki ta hanyar aminta da cewa ya sha kaye a zaben shugaban kasan da aka yi a watan jiya.

Shugabannin kasashen Afrika ukku da suka hada da Ernest Koromo na Saliyo, da Pedro Pires na Cape Verde da kuma Boni Yayi na Junhuriyar Benin sun isa Abidjan don mika wa Gbagbo bukatar ECOWAS nay a bar kujeran mulki, in kuma yaki saukar girma da arziki, tayi anfani da karfin tsiya wajen tumbuke shi.

Ana sa ran cewa shugabannin ukku zasu yi wa Mr. Gabgbo tayin bashi mafakar siyasa idan ya yarda yayi murabus. Kafin ma suje gidan shugaban kasan Gbagbo, saida shugabannin suka fara yada zango a hedkwatar rundunar sojojin kiyaye sulhu na MDD dake nan Abidjan.

Mutumen dake adawa da Gabgbo din wanda kuma kowa ya dauka shine ya lashe zaben, Alassane Ouattara ya yi kira da mutanen Cote d’Ivoire suyi yajin aiki don yilastawa hinjararren shugaban sauka, amma ga alama wannan kiran nashi bai ratsa mutanen kasar ba don kuwa duk kasuwanni, hard a nab akin tituna, suna bude, mutane na ta ci gaba da m’uamilarsu da juna.

Wasu ma’aikatan sunce su kam ba zasu iya jurewa kin zuwa wurin aiki ba.

XS
SM
MD
LG