Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe fiye da mutane 170 a tashin hankalin da ya biyo bayan zaben da ake gardamar sakamakonsa a kasar Ivory Coast


Dakarun Majalisar Dunkin Duniya suna sintiri kan titunan birnin Abidjan, Ivory Coast, Dec 22, 2010
Dakarun Majalisar Dunkin Duniya suna sintiri kan titunan birnin Abidjan, Ivory Coast, Dec 22, 2010

Ma’aikatan diflomasiyya a Majalisr Dinkin Duniya sun ce an kashe mutane fiye da 170 a tashin hankalin da ya biyo bayan zaben da ake gardamar sakamakonsa a kasar Ivory Coast

Ma’aikatan diflomasiyya a Majalisar Dinkin Duniya sun ce an kashe mutane fiye da 170 a tashin hankalin da ya biyo bayan zaben da ake gardamar sakamakonsa a kasar Ivory Coast. Suka ce an samu rahotannin da aka tabbatar da sahihancinsu, da kuma matakai na ganawa mutane azaba ko cin zarafinsu. An tattauna lamarin na kasar Ivory Coast a lokacin wani zama na Hukumar Kare hakkin Bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya yau alhamis a Geneva. Jiya laraba, Amurka ta ce tana tattaunawa da kasashen Afirka kan daukar matakin kara yawan sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisr Dinkin Duniya su dubu 10 da yanzu suke kasar Ivory Coast a yayin da wannan rikicin siyasa ke ci gaba da wakana. Jami’an gwamnatin Amurka suka ce makasudin kara yawan sojojin kiyaye zaman lafiyar ba wai kawar da shugaba Laurent Gbagbo da ya ki sauka daga kan mulki ba ne, sai dai a yi amfani da su wajen hana shi yin amfani da sojojinsa domin ci gaba da zama kan kujerar mulki. Mr. Gbagbo dai ya ki sauka daga kan mulki duk da matsin lamba daga kasashen Afirka da na yammacin duniya wadanda suka amince da abokin hamayyarsa Alassane Ouattara a zaman wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan da ya shige. Shugabannin kasashen Afirka ta Yamma sun shirya taron kolin gaggawa gobe jumma’a domin tattauna rikicin na Ivory Coast. Mr. Gbagbo ya hau gadon mulkin Ivory Coast tun shekara ta dubu biyu. Wa’adinsa ya kare tun shekarar dubu biyu da dari biyar amma sai ya ci gaba da zama kan kujerar shugabanci a saboda jinkirta zaben da aka

XS
SM
MD
LG