Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tawagar kungiyar ECOWAS na shirin yiwa shugaban kungiyar Goodluck Jonathan bayanin ganawarsu da Laurent Gbagbo


Shugabannin kasashen yammacin Afrika suna ganawa da shugaban kasar Ivory Coast. Laurent Gbagbo.
Shugabannin kasashen yammacin Afrika suna ganawa da shugaban kasar Ivory Coast. Laurent Gbagbo.

Tawagar kungiyar ECOWAS na shirin yiwa shugaban kungiyar Goodluck Jonathan bayanin ganawarsu da Laurent Gbagbo.

Tawagar shugabannin kasashen yammacin Afirka suna shirin yiwa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan bayani, kan kokarinsu na shawo kan shugaba Laurent Gbagbo ya mika mulki cikin ruwan sanyi. Yau Laraba shugabannin kasashen Benin,Cape Verde,da kuma Saliyo, zasu gana da shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a Abuja.Shugaban Najeriyan ne kuma shugaban kungiyar raya tattalain arzikin kasashe dake yammacin Afirka ta ECOWAS, wacce tace tilas Gbagbo ya sauka ko kuma ya fuskanci matakin soji daga kungiyar.Tawagar data kunshi shugabannin kasashe ukun ta gana da Mr. Gbagbo jiya Talata a fadar gwamnati inda ta bukaci yayi na’am da sakamakon zaben kasar da aka yi cikin watan jiya.Kasashen Duniya duk sun karbi sakamakon zaben kasar da ya nuna abokin takararsa Alassane Ouattara ne ya lashe zaben.Tawagar bata bada wata sanarwa ba,a yammacin jiya Talata bayan ta gana da Mr. Ouattara.Sai dai shugaban Benin Boni Yayi, yace komi ya tafi yadda ya kamata.

XS
SM
MD
LG