Rahotanni dake fitowa daga Afirka ta yamma na cewa shugabannin kasashen Afirka uku na shirin tattaki zuwa Abidjan,babban birnin kasar Ivory Coast,domin shaidawa shugaba dake kan kujerar mulki a yanzu laurent Gbagbo, da ya sauka saboda rikicin fas ya biyo bayan zaben da aka kammala.
Ministan harkokin wajen Jumhuriyar Benin,Jean Marie Ehouzou,ne ya bayyana haka ga manema labarai jiya Asabar cewa ranar talata idan Allah ya kaimu ne shugabannin kasashen jamhuriyar Benin,da na Laberia,da Cape Verde zasu isa Ivory Coast.
Wani mai magana da yawun gwamnatin Mr. Gbagbo yace barazanar da shugabannin kasashe dake cikin kungiyar ECOWAS suka yi ranar jumma'a na amfani da karfin soja su tumbuke Gbagbo bashi kan doka,don haka soki burutsune ce kawai.