Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dinkin Duniya ta Kara Tsawon Wa'adinta a Ivory Coast


'Yan sandan Ivory Coast masu goyon bayan Shugaba Laurent Gbagbo na arangama da magoya bayan Alassane Ouattara
'Yan sandan Ivory Coast masu goyon bayan Shugaba Laurent Gbagbo na arangama da magoya bayan Alassane Ouattara

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya jefa kuri’ar amincewa da tsawaita wa’adinsa na tabbatar da zaman lafiya a Ivory Coast

Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya jefa kuri’ar amincewa da tsawaita wa’adinsa na tabbatar da zaman lafiya a Ivory Caost, kwana biyu bayan da shugaba mai ci Laurent Gbagbo ya nemi sojojin tabbatar da zaman lafiya su fice daga kasar.

A wata shawarar da ya yanke jiya Litini a birnin New York, Kwamitin ya kara wa’adin sojojin tabbatar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya da wata shida, wato har zuwa karshen watan Yuni. Shawarar ta kuma yi kira ga dukkannin bangarorin su amince da Alassane Ouattara a matsayin Shugaban Ivory Coast.

Mr. Ouattara ne al’ummar duniya ta tabbatar ya ci zaben shugaban kasan da aka gudanar a watan jiya, to amman Mr. Gbagbo ya ki mika ragamar iko.

A birnin Washington, Kakakin Fadar White House Robert Gibbs ya ce a shirye Amurka ta ke ta kakaba wa Mr. Gbagbo takunkumi, kuma lokaci ya yi da yakamata ya tafi.

Tun da safiyar jiya Litini, Majalisar Dinkin Duniya ta ce wasu mutane dauke da makami sun yi ta tozarta jami’an Majalisar Dinkin Duniya a gidajensu.

Shugabar Kwamitin Tsaron Majalisar Dinkin Duniya Jakadiyar Amurka Suzan Rice, ta yi gargadin cewa duk fa wanda ya kai hari kan fararen hula ko kuma sojojin tabbatar da zaman lafiya zai gurfana gaban shar’a. Ta kuma yi kira ga mutanen Ivory Coast su kai zuciya nesa, su natsu su kuma ki yarda a ingiza su.

Jami’an Majalisar Dinkin Duniya sun ce wasu mutane dauke da bindigogi kuma saye da kayan soji sun sace dururuwan mutane, kuma an kasshe sama da mutane 50 aka kuma raunata fiye da 200 tun daga ranar Alhamis.

Tarayyar Turai dai ta ce Mr. Gbagbo da matarsa na daga cikin mutane 19 da za su fuskanci takunkumi sanadiyyar wannan danbarwa ta shugabanci. Ana kyautata zaton takunkumin zai hada da hana amfani da dukiyar da aka adana da kuma Visar tafiye-tafiye.

XS
SM
MD
LG