Za'a gudanar da zaben a jihohi shida ciki har da jihar California, jihar da ta fi kowace jiha yawan jama'a a nan Amurka.
Zaben da za'a yi ko tantama babu zai amsa tambayar, wanene zai zama zakara tsakanin Hillary Clinton da Berni Sanders, wadanda kowane ke kokarin ganin jam'iyyar Democrat ta tsayar dan takarar shugaban kasa.
Tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta doke Sanders a zaben da aka yi a Puerto Rico jiya Lahadi. Sauran kiris Hillary ta samu kuri'un da ake bukata na tsayar da ita 'yar takarar shugaba.
Kidigddigar jin ra'ayi ya nuna cewa ana keke da keke tsakanin Hillary Clinton da Bernie Sanders a jihar California. Duk da haka duka 'yan takarar biyu sun maida hankali wajen caccakar Donald Trump wanda ake kyautata zaton jam'iyyar Republican zata tsayar dan takararta na shugaban kasa.
A makon jiya Hillary Clinton ta baiyana Trump a zaman mutumin da bashi da alkibla.
Shi kuma Bernie Sanders ya baiyana Trump a zaman mutumi wanda idan bai san abun da zai fada sai ya nemi wanda zai dorawa laifi.