Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump da Clinton sun lashe zaben fidda gwani a New York na shiga takarar shugaban Amurka


Hamshakin attajirin nan Trump na Republican da Clinton ta Democrats su ne suka lashe zaben fidda gwani na jihar New York
Hamshakin attajirin nan Trump na Republican da Clinton ta Democrats su ne suka lashe zaben fidda gwani na jihar New York

Hamshakin attajirin nan- Donald Trump, da tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton sun sami nasara a zaben fidda 'yan takara da aka yi jiya Talata a jihar New York dake arewa maso gabashin Amurka.

Sun fadada ratar dake tsakaninsu da abokan takararsu, a yunkurin samun zama 'yan takarar shugabancin Amurka na jam'iyun Republican da kuma Democrat.

Bayan an kidaya kusan dukkan kuri'u, Trump ya sami gagarumar nasara da kusan kashi 60 cikin dari, idan aka kwatanta da kashi 25 cikin dari, da gwamna John Kasich, na jihar Ohio ya samu, shi kuma sanata Cruz, ya sami kashi 15 cikin dari. yayinda Madam Clinton ta doke senata Bernie Sanders da kashi 57 cikin dari, sanders kuma da ya sami kashi 42 cikin dari.

Bisa dukkan alamu Trump ne zai lashe dukkan wakilai 95 na jihar New York, wanda zai bashi wakilai 835 bayan zaben na jiya Talata. Akwai bukatar wanda zai zama dan takarar jam'iyyar Republican ya sami wakilai 1,237, matakin da ake gani da wuya Donald Trump, ya samu, kamin nan da babban taron jam'iyyar, cikin watan Yuli.

Ita kuma Madam Clinton kamin zaben na jiya Talata, tana da wakilai 1,758, da nasarar da ta samu a New York, yanzu kusan tana da wakilai 1,900, shi kuma senata Sanders, yana da wakilai ko delegates 1,185.

Jam'iyyar Democrat tana bukatar wanda zai yi mata takara ya sami ko ta sami nasarar samun wakilai 2,383 a zabukan share fage da ake yi.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:02:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG