Da yake magana ga magoya bayansa dazun nan, ya ayyana cewa "zaben fidda gwanin ya kare," kuma shine mutumin da zai sami tutar yiwa jam'iyyar Republican takara.Bayan zaben nan jiya talata, Trump ya sami wakilai 950 cikin 1,237 da ake bukata domin zama dan takara. Babu tabbas zai samu sauran wakilan nan da lokacinda uwar jam'iyyar zata yi babban taronta cikin watan Yuli.
Hakanan tashoshin talabijin sun ayyana Hilarry Clinton ta lshe hudu daga cikin jihohin nan biyar, watau Maryland, Pennsylvania, Delaware,da Connecticut. Abokin karawarta, Sanata Bernie Sanders, ya sami nasarar lashe jihar Rhode Island.
Kamin zaben na jiya Talata, Clinton tana da wakilai ko delegates 1,944. A jam'iyyar Democrat ana bukatar wakilai 2,383 kamin a ayyana mutum ya zaman wanda ya sami yiwa jam'iyyar takarar shugabancin Amurka.
Clinton ta gayawa gungun magoya bayanta a Philadelphia cewa, zata yi aiki domin hada kan jam'iyyar domin ta cimma nasara a babban zaben kasar cikin watan Nuwamba.