Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump da Sanders Suna Kokakrin Yin Muhawara Wadda Ta Sabawa Al'ada


Donald Trump na jam'iyyar Republican
Donald Trump na jam'iyyar Republican

Da alamun za'a sami canji daga ala'dar da aka saba tsakanin jam'iyun siyasar Amurka, inda 'yan takara a jam'iyya daya zasu yi ta muhawara tsakaninsu, har sai ko wace jam'iyya ta fidda dan takara.

Sai dai Donald Trump, wanda ya bayyana cikin wani shirin talabijin na ban dariya a daren Laraba, lokacinda yake amsa tambayar mai gabatar da shirin cewa, ganin Hillary taki tayi wani sabon mukabala da abokin takararta Bernie Sanders, shi zai yi muhawarar da Senata Sanders? Domald Trump ya kada baki yace ai kuwa, amma bisa sharadin cewa kudade da za'a samu daga tallace tallace a muhawarar su kai dala miliyan 10, wadanda watakil a yi amfani da su wajen tallafawa kiwon lafiyar mata.

Trump yace "ina sha'awar yin muhawara da Bernie,". "Matsala daya idan muka yi mukabala, zan kada shi."

An nasa martani ta shafinsa a dandalin Twitter a internet, Senata Bernie Sanders yace, ya amsa goron gayyata, na yin muhawara da Trump a jihar California, gabannin zaben fidda gwani da za'a yi a jihar ranar 7 ga watan Yuni.

Bernie Sanders na jam'iyyar Democrat
Bernie Sanders na jam'iyyar Democrat

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG