Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sanders Na Karfafa Fada da Shugabannin Jam'iyyar Democrats


Sanata Bernie Sanders dake neman jam'iyyarsa ta Democrats ta tsayar dashi dan takararta na shugaban kasa
Sanata Bernie Sanders dake neman jam'iyyarsa ta Democrats ta tsayar dashi dan takararta na shugaban kasa

A kokarin da yake yi na ganin shi jam'iyyar Democrats ta tsayar maimakon abokiyar hamayyarsa wadda take gaba dashi nesa ba kusa ba, yana cigaba da fada da shugabannin jam'iyyar da nufin kawar dasu daga kujerunsu

Sanata Sanaders ya zargi shugabannin jam'iyyarsu da yin kokarin nada abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton ta bayan fage ta zama 'yar takararsu.

A wasu jerin muhawara da ya dinga yi ta kafofin talibijan jiya Lahadi Sanders ya amince yana da jan aiki a gabansa kafin ya kamo Hillary Clinton. Yace idan har shi ya zama shugaban kasa to ko shakka babu zai tunbuke Debbie Wasserman Schultz shugabar jam'iyyar Democrat ta yanzu ya maye gurbinta da wani shehun malami Tim Canova wanda yake kalubalantarta a zaben 'yan majalisar wakilai da zasu fito daga jihar Florida a fafatawar fidda gwani da zasu yi a watan Agusta. Wanda ya ci shi ne zai tsaya wa jam'iyyar a zaben 'yan majalisar wakilan kasar.

Sanata Sanders yace Wasserman Schultz ba irin shugabar da ta dace da jam'iyyarsu ba ce. Ya zargi jam'iyyar da bin attajirai tana karban kudade daga wurinsu lamarin da shi Sanders ya kyama. Yace ya kamata su gayawa talakawa cewa suna tare dasu ba su dinga bin masu hannu da shuni ba.

Duk da kalamun Sanata Sanders ita Wasserman tace zata kasance cikin 'yan baruwanmu a zaben fidda gwani. Ma'ana, ba zata sa baki ba sai abun da masu zabe suka tsayar.

Tuni dai Hillary Clinton tace tana ganin kanta a matsayin wadda zata lashe zaben fidda gwani kuma ta soma shirin kalubalantar Donald Trump wanda bisa alamu shi zai zama dan takarar jam'iyyar Republican.

Mrs Hillary Clinton 'yar takarar jam'iyyar Democrats dake kan gaba
Mrs Hillary Clinton 'yar takarar jam'iyyar Democrats dake kan gaba

XS
SM
MD
LG