Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump ne ke kan gaba a jihar Indiana cikin 'yan Republican


Donald Trump dake kan gaba a jam'iyyar Republican
Donald Trump dake kan gaba a jam'iyyar Republican

Wani sabon bin ra'ayin masu kada kuri'a da aka yi a nan Amurka ranar Lahadi ya nuna Donald Trump hamshakin attajirin nan na jam'iyyar Republican dake kan gaba a zaben fidda gwani yana kara kutsawa gaba gaba a jihohin tsakiyar kasar kamar jihar Indiana inda zasu gudanar da zabe gobe.

Harsashen da jaridar NBC da mujallar Wall Street da ta Marist suka yi ya nuna Trump ne kan gaba da kashi 49 cikin dari tsakanin 'yan takarar uku na 'yan Republican inda an kwatanta da kashi 34 da Sanata Ted Cruz yake dashi da kuma kashi 13 na John Kasich wanda shi ne gwamnan jihar Ohio yanzu.

Masu nazari akan siyasar Amurka suna ganin takarar da za'a yi a jihar Indina, jihar dake da masu ra'ayin mazan jiya da dama, da take da kasar noma mai dimbin yawa, wadda kuma cibiyar ma'aikatu ce, ita ce dama ta karshe da Cruz ko Kasich suke dashi na takawa Trump birki domin kada ya lashe zaben zama dan takarar jam'iyyarsu.

Trump wanda attajiri ne kuma da ya taba aikin talibijan, amma bai taba rike mukamin siyasa ba shi ne yake kan gaba da wakilai da dama fiye da masu hamayya dashi. Trump zai je taron koli na jam'iyyar da za'a yi a watan Yuli da wakilai da dama inda jama'iyyar zata fitar da dan takararta.

A zaben baya bayan nan da aka yi a jihohi shida Trump ne ya lashe zaben da babbar tazara inda ya doke sauran 'yan takarar biyu. Ya lashe zabe a jiharsa ta New York, kana ya lashe na jihohi biyar dake makwaftaka da jihar. Za'a ga yadda zata kaya a jihohi tara da suka rage bayan zaben Indiana da za'a yi gobe.

XS
SM
MD
LG