Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump da Sanders sun lashe zaben fidda gwani a jihar West Virginia


Donald Trump na jam'iyyar Republican
Donald Trump na jam'iyyar Republican

Manyan tashoshin talabijin na Amurka sun ayyana cewa Senata Bernie Sanders na jihar Vermont, da kiris ya kada tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton a zaben fidda gwani na masu takarar shuganacin Amurka da aka yi jiya Talata a jihar West Virginia.

Sanders, zai sami karin wakilai 13, duk da haka bashi da wata hanyar wuce gaban Hillary Clinton wacce take can gaba da shi nesa ba kusa ba, a yawan wakilai.

A farkon shekaran nan ne Madam Clinton ta fusatar 'yan jihar West Virginian lokacinda tace, "zata sa masu aikin hako gawayin Coal da kamfanonisu su rasa ayyukan yi."

Sana'ar hakar gawayin Coal yana tattare da hadari kuma gashi da gurbata yanayi a zaman makamshi, amma wani bangaren jihar Virginia ya dogara kan sana'ar.

Makon jiya, Madam Clinton ta nemi gafara daga masu zabe a jihar, tana cewa, ina so ku sani cewa zan yi iya karfi na in taimakawa wadanda koma bayan aiki da gawayin Coal ya shafa."

Sai dai a bangaaren 'yan Republican bata sake zani ba, mutuminda ake jin shine dan takarar jam'iyyar Donald Trump shine ya lashe zaben na West Virginia da kuma jihar Nebraska.Tuni ma ya maida hankali wajen zaben mutuminda zai dauka a zaman mataimakin shugaban kasa.

Bernie Sanders na jam'iyyar Democrats
Bernie Sanders na jam'iyyar Democrats

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG