Amma tana fuskantar kalubale mai tsanani a jihar California, daga mutum daya da ya rage yana karawa da ita, watau Senata Bernie Sanders na jihar Vermont.
Madam Clinton wacce take kokarin zama mace ta farko da zata shugabanci Amurka kamin babban taron jam'iyyar a watan Yuli, yanzu tana da wakilai dubu biyu da dari uku da goma, cikin wakilai dubu biyu d a dari uku da tamanin da uku da ake bukata domin ta zama mace ta farko da wata babbar jam'iyyar siyasa a Amurka zata tsayar takarar shugabancin kasa. Babban abokin hamayyarta Bernie Sanders yana da wakilai 1,542.
A wani lamari kuma,alkalin wata babbar kotun Amurka ya bayyana kasidu fiyeda 400 dangane da yadda ma'aikatan tsohuwar jami'ar Trump suke amfani da matakai masu gauni na sa mutane su shiga jami'ar domin koyon dabarun sayen gidaje da wasu kadarori.
Sakin bayanan, wani bangare ne na shari'ar da wasu suka shigar suna zargin an yi musu zamba.
A wani taro da manema labarai a ofishinsa dake New York jiya Talata ya ci gaba da zargin alkalin da ya yanke shari'ar da cewa alkalin bashi da adalci.