A binciken da ofishin ya gudanar a ma'aikatar harkokin wajen Amurka inda Hillary Clinton tayi aiki a matsayin Sakatariyar Harkokin Waje ya sameta da laifin yin anfani da nata email a ayyukan gwamnati lamarin da ya sabawa tsarin ma'aikatar.
Yau ya kamata ofishin ya bada rahoton sakamakon binciken amma kwatsam ba zato sai ma'aikatar harkokin wajen ta kira taron manem labarai jiya Laraba tana amsa tambayoyi akan abubuwan masu bincike suka gano. Yayin bada amsoshin ne suka ambato batun Hillary Clinton da yin anfani da nata email wurin aiwatar da ayyukan gwamnati.
Jami'an binciken suka ce babu wata shaida cewa Hillary Clinton ta nemi izini kafin ta soma anfani da email dinta ta aiwatar da ayyukan da suka shafi gwamnatin kasar kamar yadda doka ta bukaci ta yi.
Yin anfani da kafofin da gwamnati ta amince dasu ka iya hana masu satar bayanai ta yanar gizo daga samun nasara.
Shi dai wannan rahoton bai cimma wata matsaya ba akan dalilin da ya sa Hillary Clinton bata nemi izini ba. To saidai an ce babu wata doka takamaimai da ta hana yin anfani da email din karan kai idan aka bi tsarin matakan tsaro.
Mrs. Hillary Clinton ita ce take kan gaba a zaben fidda gwani a jam'iyyar Democrat a kokarinta na neman shugabancin kasar Amurka.