Babban magatakardan Majalisar DinkinDuniya Ban ki-moon ya ki amincewa da bukatar shugaban Ivory Coast wanda ke tsaka mai wuya cewa sojojin kiyaye zaman lafiya na majalisar su fice daga cikin kasar.
Cikin sanarwa da ya bayar, Mr Ban yace ofishin majalisar dake Cote‘Dvoire, zai kammala aikinsa kuma ya ci gaba da sa ido kuma ya tara bayanai kan keta hakkin bail’adama,zuga mutane su tada tarzoma,da kuma kai wa sojojin kiyaye zaman lafiyan hari.
Asabar ce Mr. Gbagbo ya umurci sojojin kiyaye zaman lafiya su bar kasar saboda wai suna goyon bayan ‘yan tawaye dake goyon bayan abokin hamayyarsa Alassane Ouattara.
Kasashen Duniya sun yi na’am da Mr.Ouattara a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi cikin watan jiya,amma Mr.Gbagbo ya ki ya mika mulki.
Mr. Gbagbo yana ci gaba da fuskantar matsin lamba,ranar jumma’a ce shugaban Faransa Nicolas Sarkozy ya yi kashedi ga Mr.Gbagbo cewa ya mika mulki nan da karshen makon nan,ko kuma tarayyar Turai ta aza wa kasar takunkumi.
Frayin MinistanKenya Ra'ila Odinga,yace tilas tarayya Afirka ta shirya amfani da karfi wajen tilastawa Mr.Gbagbo ya mika mulki domin tabbatarda makomar Demokuradiyya.