Majalisar dokokin Kenya ta bukaci kasar da ta janye daga yarjejeniyar da ta kafa kotun bin kadin manyan laifuffuka ta duniya, ko ICC a takaice. A kuri’ar da kusan dukkan ‘yan majalisar dokokin sun amince da ita, wakilan sun bukaci gwamnati da ta tsame hannunta daga yarjejeniyar Rome da ta kafa kotun ta ICC. Wannan kuduri wani mataki ne na yunkurin hana kotun yin shari’ar wasu ‘yan Kenya su shida da ake zargi da kitsa tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shekata ta dubu biyu da takwas a kasar. A makon jiya babban mai gabatar da kararraki na kotun ICC, Luis Moreno-Ocampo, ya bayyana wadannan ‘yan Kenya su shida ya kuma bukace su da su bayyana domin radin kansu a gaban kotun dake birnin Hague. Ya zamo tilas karkashin doka Kenya ta hada kai da wannan kotun a zaman daya daga cikin kasashen da suka sanya hannu a kan yarjejeniyar kafa ta. A lokacin muhawarar da ‘yan majalisar dokokin Kenya suka yi jiya laraba kan wannan batu, dan majalisa kuma ministan makamashin Kenya, Kiraitu Murungi ya bayyana kotun a zaman wani makami na mulkin mallakar kasashen yammacin duniya. Ya lura cewa tun lokacin da aka kafa wannan kotu, ‘yan Afirka ne kadai daga kasashen da turawa suka yi wa mulkin mallaka ake gurfanar da su gabanta.
Majalisar dokokin Kenya ta bukaci kasar da ta janye daga yarjejeniyar da ta kafa kotun bin kadin manyan laifuffuka ta duniya
Majalisar dokokin Kenya ta bukaci kasar da ta janye daga yarjejeniyar da ta kafa kotun bin kadin manyan laifuffuka ta duniya.