Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Boko Haram Da Martanin Jami'an Tsaro


Mota Mai Sulke a helkwatar rundunar tsaro ta hadin guiwa a Maiduguri, Najeriya.
Mota Mai Sulke a helkwatar rundunar tsaro ta hadin guiwa a Maiduguri, Najeriya.

Masu rajin kare hakkin Bil-Adama da kwararru kan harkoki da suka shafi Najeriya, suna kira da a yi takatsan tsan kan martanin tsaro da za a dauka sakamakon munanan hare hare a arewacin Najeriya, da ake dora alhakinsa kan masu tsatstsauran ra’ayin Islama.

Masu rajin kare hakkin Bil-Adama da kwararru kan harkoki da suka shafi Najeriya, suna kira da a yi takatsan tsan kan martanin tsaro da za a dauka sakamakon munanan hare hare a arewacin Najeriya, da ake dora alhakinsa kan masu tsatstsauran ra’ayin Islama. Kwararru suna gargadin idan aka dauki gurguwar shawara a martanin da aka dauka, hakan yana iya janyo karin fitina.

Kungiyar kare hakkin Bil-Adama ta Human Rights watch tana kira ga hukumomin Najeriya su dauki mataki nan take na hukunta abin da ta kira “mummunan laifi” da ya halaka akalla mutane dari a jihar Yobe dake arewacin Najeriya, ranar 4 ga watan Nuwamban nan.

Wadanda ake azawa laifin wan nan danyen aiki, sune ‘yan wata kungiyar masu tsatstsauran ra’ayin Islama da hukumomi da kafofin yada labarai a Najeriya suke kira, Boko Haram.

‘Ya’yan wan nan kungiya suna son ganin an kafa tafarkin shari’a a jihohi dake arewacin Najeriya. Sun ce zasu ci gaba da kai farmaki har sai jami’an tsaron sun daina cin zarafin ‘yan kungiyar da kuma talakawa farar hula.

A cikin sanarwa da ta bayar cikin wan nan mako, kungiyar Human Rights watch, tace ana zargin kungiyar da hare hare da suka kai ga kashe mutane 425 a cikin wan nan shekara, mutanen da aka kashe sun hada da ‘Yansanda, sojoji, shugabannin siyasa dana al’uma,malaman addinin Islama,pastoci da mabiya addinin kirista.

Kungiyar Human Rights watch tana kuma gargadin kan wuce makadi da rawa daga jami’an tsaro. An kashe daruruwan mutane a wasu matakan murkushe mayakan sakan a 2009. Tun lokacin kungiyar tace tana da shaidar an kashe daruruwan mutane ba tareda izini ba.

William Minter,wadda editan wata mujalla a internet, da ake kira Afirka Focus, yana sa ido sosai kan harkokin Najeriya. Yace tilas ne jami’an tsaron Najeriya su fahimci cewa matakan da suke dauka suna iya zama daya daga cikin matsaloli dake ruruta al’amarin:

“Idan kuka kashe wasu mutane, ko kuka kama wasu, hakan yana iya kara gibi tsakaninku da sauran jama’a baki daya,wadda zai iya taimakawa irin wadan nan kungiyoyi su kara samun magoya baya, wadan nan matakai babu abinda zasu haifar illa kara iza wutar rikicin,yayinda ake banza da ainihin dalilanda suka janyo rikicin tun fil azal”.

Najeriya ta dauki matakan hukunta jami’an tsaro da ake zargi da cin zarafin Bil-Adama. A farkon shekaran nan

Gwamnati ta gurfanar da ‘yansanda biyar kan zargin kashe shugaban ‘yan Boko Haram Mohammed Yusuf, da wasu mabiyansa.

Baya ga haka kwararru suka ce akwai bukatar gwamnati ta dauki kwararan matakai na tunkurar talauci da cin hanci da rashawa, wadanda suka janyo fitinar da goyon bayan da masu matsanancin ra’ayin suke samu daga jama’a dake yankin. John Campbell, wadda ke nazari da rubuce rubuce kan Najeriya a cibiyar harkokin ketare dake nan Amurka, yace mutane suna cike da fushi:

“Abinda yake faruwa shine an shiga wani kazamin yanayi, ko kuma muce bore wadda yake nuna talaucewar arewacin Najeriya. Kuma a ganina akwai gibi tsakanin yankin da gwamnati dake Abuja, wacce ake yi wa kallon kamar bata ma damu da su ba”.

Zanga zanga ya barke a wasu sassan arewacin Najeriya bayan zaben shugaban kasa cikin watan Afrilu da shugaban kasa Goodluck Jonathan, daga kudancin kasar mai arzikin mai ya sami nasara. Haka ma kudancin kasar ta fafata na shekaru daga kungiyoyin mayakan sakai dake korafin cewa babu adalci a yadda ake rabon arzikin mai.

Paul Lubeck, masanin zamantakewar siyasa kuma gwani kan harkokin kungiyoyin masu matsanancin ra’ayin addini a arewacin Najeriya, wadda yake tare da jami’ar California dake Santa Cruz, yace abinda arewacin Najeriya take bukata shine sake farfado da masanantunta ,wadanda suka yi aiki har sai zuwa wajajen 1980,baya ga haka kuma a fara noman shinkafa:

“Duk wan nan yana bukatar shiri na sake farfado da tattalin arzikin arewacin Najeriya da zai amfani kasar kuma ya baiwa matasa madafa. Domin idan lamarin yaci gaba da tabarbarewa, za a ci gaba da samun turjiya, da tsoma hanun jami’an tsaro wadda hakan zai kara ruruta lamarin”.

Duka jami’an biyu,Lubeck da Campbell, suna ganin Amurka tana da rawa da zata taka, ganin ita Amurkan ta bayyana damuwar ganin arewacin Najeriyar ta fara zama kamar sassa dake hanun al-Shabab na Somalia. Duka jami’an biyu sun jaddada cewa matakan difilomasiyya da horaswa daga Amurka zasu taimakawa gwamnatin shugaba Jonathan ta tunkari matsalar da matakan soji kadai ba zasu iya warwarewa ba.

Aika Sharhinka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG