A karo na biyu, sanannen marubucin nan dan Najeriya, Chinua Achebe, ya ki karbar lambar yabon da gwamnatin kasarsa ta ba shi.
Marubucin, wanda yayi suna a duniya da littafinsa mai suna “Things Fall Apart” yana cikin ‘yan Najeriya da aka yi niyyar ba ma lambar yabo ta kasa da ake kira C.F.R. (Commander of the Order of the Federal Republic) a wurin wani buki jiya litinin.
Amma Achebe, wanda a yanzu yake zaune a Amurka, ya ce Najeriya ba ta takala ko magance batutuwan da ya ambata a lokacin da ya ki karbar irin wannan lambar yabon a baya a shekarar 2004 ba. A wancan lokacin, Achebe ya rubuta ma shugaba Olusegun Obasanjo wasika yana fadin cewa Najeriya tana fama da rashin tsaro da kuma zarmiya da cin hanci, kuma wasu sassan kasar, ciki har da jihar shi marubucin ta Anambra, sun zamo kamar gidan sarautar wasu ‘yan tsiraru da ba su bin doka.
Wani kakakin shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana shawarar marubuci Chinua Achebe ta kin karbar wannan lambar yabon a zaman abin takaici. Ya ce Achebe ya kasa lura da irin sauyi mai yawa da aka yi ga tsarin zabe a kasar karkashin mulkin Mr. Jonathan, ya kuma ce watakila dalilin hakan shi ne don marubucin ba ya zaune a Najeriya ne.